1. A halin yanzu, yunwa ta tsananta a ƙasar.
2. Sa'ad da suka cinye hatsin da suka kawo daga Masar, mahaifinsu ya ce musu, “Ku koma, ku sayo mana ɗan abinci.”
3. Amma Yahuza ya ce masa, “Mutumin fa, ya yi mana faɗakarwa sosai, ya ce, ‘Idan ba tare da autanku kuka zo ba, ba za ku ga fuskata ba.’
4. In za ka yarda ka aiki ɗan'uwanmu tare da mu, sai mu gangara mu sayo muku abinci.