Far 32:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Yakubu ya yi tafiyarsa, mala'ikun Allah kuma suka gamu da shi.

2. Sa'ad da Yakubu ya gan su ya ce, “Waɗannan rundunar Allah ce!” Saboda haka ya sa wa wannan wuri suna Mahanayim.

3. Yakubu kuwa ya aiki jakadu a gabansa zuwa wurin Isuwa ɗan'uwansa a cikin ƙasar Seyir a karkarar Edom,

4. yana umartarsu da cewa, “Haka za ku faɗa wa shugabana Isuwa, ‘Ga abin da baranka Yakubu ya ce, “Na yi baƙunta a ƙasar Laban, na zauna har wa yau.

5. Ina da takarkarai, da jakai, da garkuna, da barori mata da maza, na kuwa aika a faɗa wa shugabana domin in sami tagomashi a idonka.” ’ ”

6. Jakadun kuwa suka komo wurin Yakubu, suka ce, “Mun je wurin ɗan'uwanka Isuwa, yana kuwa zuwa ya tarye ka da mutum arbaminya tare da shi.”

7. Yakubu fa ya tsorata ƙwarai, ya damu, sai ya karkasa mutanen da suke tare da shi, da garkunan tumaki da awaki, da na shanu, da raƙuma cikin ƙungiya biyu,

8. yana tunani cewa, “In Isuwa ya zo ya hallaka ƙungiya guda, ƙungiyar da ta ragu sai ta tsira.”

Far 32