Far 14:16-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Sai ya washe kayayyakin duka, ya kuma ƙwato ɗan'uwansa Lutu da kayayyakinsa da mata da maza.

17. Sai Sarkin Saduma ya fita ya taryi Abram sa'ad da ya komo daga korar Kedarlayomer da sarakunan da suke tare da shi, a Kwarin Shawe, wato Kwarin Sarki.

18. Sai Malkisadik Sarkin Salem, wato Urushalima, ya kawo gurasa da ruwan inabi. Shi firist ne na Allah Maɗaukaki.

19. Ya kuwa sa wa Abram albarka ya ce, “Shi wanda ya yi sama da ƙasa, Allah Maɗaukaki ya sa wa Abram albarka.

20. Ga Allah Maɗaukaki yabo ya tabbata, shi wanda ya ba ka maƙiyanka a tafin hannunka!” Abram kuwa ya ba shi ushiri na duka.

21. Sai Sarkin Saduma ya ce wa Abram, “Ka ba ni mutanen, amma ka riƙe kayayyakin don kanka.”

22. Amma Abram ya ce wa Sarkin Saduma, “Na riga na rantse wa Ubangiji Allah Maɗaukaki, wanda ya yi sama da ƙasa,

23. cewa ba zan ɗauki ko da zare ɗaya ko maɗaurin takalmi ba, ko kowane abin da yake naka, domin kada ka ce, ‘Na arzuta Abram.’

24. A ni kaina ba zan ɗauki kome ba illa abin da samari suka ci, da rabon mutanen da suka tafi tare da ni. Sai dai kuma Aner, da Eshkol, da Mamre su ɗauki nasu rabo.”

Far 14