Far 11:6-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ubangiji kuwa ya ce, “Ga su, su jama'a ɗaya ce, su duka kuwa harshensu guda ne, to fa, ga irin abin da suka fara yi, ba abin da za su shawarta su yi da zai gagare su.

7. Zo mu sauka, mu dagula harshensu, domin kada su fahimci maganar juna.”

8. Haka kuwa daga wurin Ubangiji ya warwatsa su ko'ina bisa duniya, sai suka daina gina birnin.

9. Domin haka aka kira sunan wurin Babila, domin a nan ne Ubangiji ya dagula harshen dukan duniya, daga nan ne kuma Ubangiji ya warwatsa su ko'ina bisa duniya.

10. Waɗannan su ne zuriyar Shem. Lokacin da Shem yake da shekara ɗari, ya haifi Arfakshad bayan Ruwan Tsufana da shekara biyu.

11. Shem kuwa ya yi shekara ɗari biyar bayan haihuwar Arfakshad, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.

12. Sa'ad da Arfakshad yake da shekara talatin da biyar ya haifi Shela.

13. Arfakshad kuwa ya yi shekara arbaminya da uku bayan haihuwar Shela, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.

14. Sa'ad da Shela yake da shekara talatin, ya haifi Eber,

15. Shela kuwa ya yi shekara arbaminya da uku bayan haihuwar Eber, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.

16. Sa'ad da Eber ya yi shekara talatin da huɗu ya haifi Feleg,

17. Eber kuwa ya yi shekara arbaminya da talatin, bayan haihuwar Feleg, ya kuma haifi 'ya'ya mata da maza.

18. Sa'ad da Feleg ya yi shekara talatin ya haifi Reyu.

Far 11