Ezra 3:3-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Suka ta da bagaden a wurinsa domin suna jin tsoron mutanen ƙasar. Suka miƙa wa Ubangiji hadayu na ƙonawa safe da yamma.

4. Suka kuma kiyaye Idin Bukkoki kamar yadda aka rubuta, suna miƙa hadayu na ƙonawa kowace rana bisa ga yawan adadin hadayun da ake bukata.

5. Daga baya kuma suka miƙa hadayun ƙonawa na yau da kullum, da hadayu na amaryar wata, da ƙayyadaddun hadayu na idodin Ubangiji, da hadayu na amaryar wata, da ƙayyadaddun Ubangiji.

6. Tun daga rana ta fari ga watan bakwai, suka fara miƙa wa Ubangiji hadayu na ƙonawa, amma ba a riga an aza harsashin Haikalin Ubangiji ba.

7. Sai suka ba magina da masassaƙa kuɗin, suka kuma ba Sidoniyawa da mutanen Taya abinci, da abin sha, da mai don su kawo itacen al'ul daga Lebanon zuwa teku a Yafa bisa ga izinin da suka samu daga wurin sarki Sairus.

8. A watan biyu na shekararsu ta biyu da suka komo wurin Haikalin Allah a Urushalima, sai Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, da Yeshuwa ɗan Yehozadak, da sauran 'yan'uwansu firistoci, da Lawiyawa da dukan waɗanda suka komo Urushalima daga bauta suka fara aikin ginin. Suka sa Lawiyawa 'yan shekara ashirin zuwa gaba su yi shugabancin aikin ginin Haikalin Ubangiji.

Ezra 3