Ez 41:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai ya kai ni cikin Haikalin, sa'an nan ya auna ginshiƙai. Fāɗin ginshiƙan kamu shida ne a kowane gefe.

2. Fāɗin ƙofar kamu goma ne. Madogaran ƙofar kamu biyar ne a kowane gefe. Sai ya auna Haikalin, tsawonsa kamu arba'in ne faɗinsa kuma kamu ashirin ne.

3. Sai ya shiga ɗaki na can ciki, ya auna madogaran ƙofar, ya sami kamu biyu biyu. Tsayin ƙofar kuma kamu shida ne. Faɗin ƙofar kamu bakwai ne.

4. Ya kuma auna ɗaki na ƙurewar ciki, tsawonsa kamu ashirin ne, faɗinsa kuma kamu ashirin. Sai ya ce mini, “Wannan shi ne Wuri Mafi Tsarki.”

5. Sai kuma ya auna bangon Haikalin, kaurinsa kamu shida ne. Faɗin ɗakunan da suke kewaye da Haikalin kamu huɗu ne.

6. Ɗakunan benaye ne masu hawa uku. Akwai ɗakuna talatin a kowane hawa. Akwai katanga kewaye da Haikalin don ta tokare ɗakunan, domin ba a so ɗakunan su jingina da bangon Haikalin.

7. Faɗin ɗakunan yana ƙaruwa daga hawa zuwa hawa, gama katangar da take kewaye da Haikali ta yi ta ƙaruwa daga hawa zuwa hawa. A gefen Haikalin akwai matakan hawa. Don haka ana iya hawa daga ɗaki na ƙasa zuwa hawa na uku ta hanyar hawa na biyu.

15-16. Ya kuma auna tsawon ginin da yake fuskantar farfajiyar da take wajen yamma da hanyar fita, kamu ɗari ne. Cikin Haikalin, da ɗaki na can ciki, da shirayi, dukansu uku suna da tagogi masu gagara badau. An manne bangon Haikalin da yake fuskantar shirayin da katako, tun daga ƙasa har zuwa tagogi. [Tagogin kuma an rufe su.]

17-18. An zana siffofin kerubobi da na itatuwan dabino a bangon Haikali ciki da waje har zuwa kan ƙofar shiga. Zanen siffar itacen dabino yana a tsakanin kerub da kerub. Kowane kerub yana da fuska biyu.

21-22. Madogaran ƙofofin Haikalin murabba'i ne. Akwai wani abu mai kama da bagaden itace a gaban Wuri Mai Tsarki, tsayinsa kamu uku ne, tsawonsa kamu biyu ne. Kusurwoyinsa da gindinsa, da jikinsa na itace ne. Sai ya ce mini, “Wannan shi ne tebur da yake a gaban Ubangiji.”

Ez 41