Ez 36:7-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. “Domin haka ni Ubangiji Allah na rantse, cewa al'umman da suke kewaye da ku su ma za su sha zargi.

8. Amma ku, ya duwatsun Isra'ila, za ku miƙa rassanku ku ba da amfani ga mutanen Isra'ila, gama za su komo gida ba da jimawa ba.

9. Ga shi, ni naku ne, zan juyo wurinku. Za a kafce ku, a yi shuka!

10. Zan sa dukan mutanen Isra'ila su riɓaɓɓanya a cikinku. Za su zauna cikin biranen, su gina rusassun wurare.

11. Zan sa mutum da dabba su yawaita a cikinku, su kuma ba da amfani. Zan sa a zauna a cikinku kamar dā, sa'an nan zan nuna muku alheri fiye da dā. Daga nan za ku sani, ni ne Ubangiji.

12. Zan kuma sa mutanena, Isra'ila, su yi tafiya a kanku, za ku zama gādonsu, ba za ku ƙara kashe 'ya'yansu ba.

13. “Ni Ubangiji Allah na ce, da yake mutane sukan ce muku, 'Kuna cinye mutane, kuna kuma kashe 'ya'yan al'ummarku,

14. saboda haka ba za ku ƙara cinye mutane ba, ba kuwa za ku ƙara kashe 'ya'yan al'ummarku ba. Ni Ubangiji Allah na faɗa.

15. Ba zan ƙara bari ku sha zargi wurin sauran al'umma ba, ba kuwa za ku ƙara shan kunya a gaban jama'a ba, ba kuma zan ƙara sa al'ummarku ta yi tuntuɓe ba, ni Ubangiji Allah na faɗa.”

16. Ubangiji Kuma ya yi magana da ni, ya ce,

Ez 36