Zan sa mutum da dabba su yawaita a cikinku, su kuma ba da amfani. Zan sa a zauna a cikinku kamar dā, sa'an nan zan nuna muku alheri fiye da dā. Daga nan za ku sani, ni ne Ubangiji.