Ez 20:35-42 Littafi Mai Tsarki (HAU)

35. Zan kawo ku cikin ruƙuƙin jama'a, in yi muku shari'a fuska da fuska.

36. Kamar yadda na yi wa kakanninku shari'a a jejin ƙasar Masar, haka kuma zan yi muku shari'a, ni Ubangiji Allah na faɗa.

37. “Zan sa ku wuce ta ƙarƙashin sanda, in ƙulla alkawarina da ku.

38. Zan fitar da 'yan tawaye a cikinku, da waɗanda suke yin mini laifi. Zan fito da su daga ƙasar da suke zaune, amma ba za su shiga ƙasar Isra'ila ba. Za ku kuwa sani ni ne Ubangiji Allah.

39. “Ya ku, mutanen Isra'ila, ni Ubangiji Allah, na ce, bari kowa ya tafi ya bauta wa gunkinsa daga yanzu zuwa gaba, tun da yake ba za ku kasa kunne gare ni ba, amma kada ku ɓata sunana mai tsarki da hadayunku da gumakanku.

40. “Gama a kan dutsena ne mai tsarki, wato a bisa ƙwanƙolin dutsen Isra'ila, dukan mutanen Isra'ila za su bauta mini a ƙasar, a nan ne zan karɓe su. A nan kuma zan nemi sadake-sada-kenku, da hadayunku mafi kyau.

41. Zan karɓe ku kamar turare mai ƙanshi sa'ad da na fisshe ku daga cikin sauran mutane, na tattaro ku daga ƙasashen da aka warwatsa ku. Zan nuna tsarkina a cikinku a idon sauran al'umma.

42. Za ku sani ni ne Ubangiji sa'ad da na kawo ku ƙasar Isra'ila, ƙasar da na rantse zan ba kakanninku.

Ez 20