16. Kin ɗauki waɗansu rigunanki, kika yi wa kanki masujadai masu ado, sa'an nan kika yi karuwanci a cikinsu, irin abin da ba a taɓa yi ba, ba kuwa za a yi ba nan gaba.
17. Kin kuma ɗauki kayan adonki na zinariyata da azurfata waɗanda na ba ki, kin yi wa kanki siffofin mutane don ki yi karuwanci da su.
18. Kin ɗauki tufafinki da aka yi musu ado, kika lulluɓe su, sa'an nan kika ajiye maina da turarena a gabansu.
19. Abincina da na ba ki kuma, wato lallausan gāri, da mai, da zuma, waɗanda na ciyar da ke da su, kin ajiye a gabansu don ƙanshi mai daɗi, ni Ubangiji Allah na faɗa.
20. “Kin kuma kwashe 'ya'yana mata da maza waɗanda kika haifa mini kin miƙa su hadaya ga gumaka. Karuwancinki, ba ƙanƙanen abu ba ne.
21. Kin karkashe 'ya'yana, kin sa su ratsa cikin wuta.
22. A cikin aikata dukan abubuwanki na banƙyama kuma, da karuwancinki, ba ki tuna da kwanakin kuruciyarki ba, lokacin da kike tsirara tik, kina birgima cikin jinin haihuwarki.
23. “Bayan dukan muguntarki (Kaito, kaitonki! Ni Ubangiji Allah na faɗa),
24. sai kika gina wa kanki ɗakunan tsafi a kowane fili.
25. Kika kuma gina ɗakin tsafi a kowane titi. Kin waƙala darajarki, kin ba da kanki ga kowane mai wucewa, ta haka kika yawaita karuwancinki.
26. Kin yi karuwanci da Masarawa, maƙwabtanki masu kwaɗayi. Kin yawaita karuwancinki don ki tsokani fushina.