Ez 1:21-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Idan talikan sun motsa, sai ƙafafun kuma su motsa. Idan sun tsaya cik, sai su ma su tsaya. Idan kuma talikan sun ɗaga sama, sai ƙafafun su ɗaga sama tare da su, gama ruhun talikan yana cikin ƙafafun.

22. Sama da talikan akwai kamannin al'arshi mai walƙiya kamar madubi.

23. A ƙarƙashin al'arshin fikafikansu sun miƙe kyam daura da juna. Kowane taliki yana da fikafikai biyu da su yake rufe jikinsa.

24. Sa'ad da suke tafiya, sai na ji motsin fikafikansu kamar amon ruwa, kamar kuma muryar tsawar Maɗaukaki, kamar hayaniyar runduna. Idan sun tsaya cik, sai su saukar da fikafikansu.

25. Sai aka ji murya ta fito daga saman al'arshi ɗin.

26. A saman al'arshin akwai wani abu mai kamar kursiyin sarauta da aka yi da yakutu. Akwai wani kamar mutum yana zaune a kan abin nan mai kama da kursiyin sarauta.

27. Daga kwankwasonsa zuwa sama yana walƙiya kamar tagullar da aka kewaye ta da wuta. Daga kwankwasonsa zuwa ƙasa yana haskakawa kamar wuta.

28. Kamar kamannin bakan gizo a cikin gizagizai a ranar da aka yi ruwan sama, haka nan kamannin hasken da yake kewaye da shi yake. Wannan shi ne kamannin kwatancin ɗaukakar Ubangiji. Sa'ad da na gani, sai na faɗi rubda ciki, na ji muryar wani tana magana.

Ez 1