1. A ranar biyar ga watan huɗu, a shekara ta talatin, ina cikin waɗanda aka kai su bautar talala, muna kusa da kogin Kebar, sai aka buɗe mini sammai, na kuwa ga wahayi na ɗaukakar Allah.
2. A kan rana ta biyar ga watan, a shekara ta biyar da aka kai sarki Yekoniya bautar talala,
3. Ubangiji ya yi magana da Ezekiyel, firist, ɗan Buzi, a ƙasar Kaldiyawa, kusa da kogin Kebar. Ikon Ubangiji yana bisa kansa.
4. Da na duba, sai ga hadiri mai iska ya taso daga wajen arewa, da wani babban girgije da haske kewaye da shi, da wuta tana ta ci falfal. A tsakiyar wutar wani abu yana walƙiya kamar tagulla.
5. Daga tsakiya wutar, sai ga kamannin waɗansu talikai su huɗu. Ga irin kamanninsu, suna kama da mutane.
6. Amma kowannensu yana da fuskoki huɗu, da fikafikai huɗu.
7. Ƙafafunsu miƙaƙƙu ne, tafin sawayensu yana kama da na maraƙi, suna walƙiya kamar gogaggiyar tagulla.
8. Suna kuma da hannuwa kamar na mutane a ƙarƙarshin fikafikansu huɗu. Ga yadda fuskoki da fikafikan talikai huɗu ɗin suke.
9. Fikafikansu suna taɓa juna, kowannensu ya miƙe gaba, ba su juyawa sa'ad da suke tafiya.
10. Kamannin fuskokinsu, su huɗu ɗin, kowannensu yana da fuska irin ta mutum a gaba, da fuska irin ta zaki a dama, da fuska irin ta bijimi a hagu, da fuska irin ta gaggafa a baya.
11. Suka kuma buɗe fikafikansu sama. Kowane taliki yana taɓa fiffiken ɗan'uwansa da fikafikansa biyu, da kuma fikafikansa biyu yake rufe jikinsa.