11. “Na yi ta dubawa saboda manya manyan maganganun fariya da ƙahon yake hurtawa, sai na ga an kashe dabbar, an jefar da gawar cikin wuta don ta ƙone.
12. Sauran dabbobi kuwa aka karɓe mulkinsu, amma aka bar su da rai har wani ƙayyadadden lokaci.
13. “A cikin wahayi na dare, na ga wani kamar Ɗan Mutum.Yana zuwa cikin gizagizai,Ya zo wurin wanda yake Tun Fil Azal,Aka kai shi gabansa.
14. Aka kuwa danƙa masa mulki, da ɗaukaka, da sarauta,Domin dukan jama'a, da al'ummai, da harsuna su bauta masa.Mulkinsa, madawwamin mulki ne,Wanda ba zai ƙare ba.Sarautarsa ba ta tuɓuwa.”
15. “Amma ni Daniyel raina ya damu, wahayin da na gani ya tsorata ni.
16. Sai na matsa kusa da ɗaya daga cikin waɗanda suke tsaye a wurin, na tambaye shi ma'anar waɗannan abubuwa duka. Sai ya bayyana mini, ya kuma ganar da ni ma'anar waɗannan abubuwa.
17. Waɗannan manyan dabbobi guda huɗu, sarakuna ne huɗu waɗanda za su taso a duniya.
18. Amma tsarkaka na Maɗaukaki za su karɓi mulki, su kuwa riƙe mulkin har abada abadin.
19. “Sai na nemi in san ainihin ma'anar dabba ta huɗu, wadda ta bambanta da sauran. Tana da bantsoro ƙwarai, tana kuma da haƙoran baƙin ƙarfe da faratan tagulla. Ta cinye, ta ragargaje, sa'an nan ta tattake sauran da ƙafafunta.
20. Na kuma so in san ma'anar ƙahoninta goma, da ɗaya ƙahon wanda ya tsiro, wanda aka tumɓuke ƙahoni uku a gabansa. Ƙahon nan yake da idanu da bakin da yake hurta manyan maganganun fariya, wanda girmansa ya fi na sauran.
21. “Ina dubawa ke nan sai ga wannan ƙaho yana yaƙi da tsarkaka har ya rinjaye su,
22. sai da Tun Fil Azal ya zo ya yanke shari'a, aka ba tsarkaka na Maɗaukaki gaskiya. Da lokaci ya yi aka ba tsarkaka mulkin.
23. “Ga abin da ya ce, ‘Dabba ta huɗu za ta zama mulki na huɗu a duniya, wanda zai bambanta da sauran mulkokin. Zai cinye duniya duka, ya ragargaje ta, ya tattake ta.