Dan 2:31-42 Littafi Mai Tsarki (HAU)

31. “Ya sarki, ka ga wani babban mutum-mutum mai walƙiya, mai bantsoro, yana tsaye a gabanka.

32. An yi kan mutum-mutumin da zinariya tsantsa. Ƙirji da damutsa, an yi su da azurfa, cikinsa da cinyoyinsa, an yi su da tagulla.

33. Da baƙin ƙarfe aka yi sharaɓansa, an yi ƙafafunsa da baƙin ƙarfe gauraye da yumɓu.

34. Sa'ad da kake cikin dubawa, sai aka gutsuro wani dutse ba da hannun mutum ba, aka bugi ƙafafunsa na baƙin ƙarfe gauraye da yumɓu, aka ragargaza shi.

35. Sa'an nan baƙin ƙarfen, da yumɓun, da tagullar, da azurfar, da zinariyar suka ragargaje gaba ɗaya, duka suka zama kamar ƙaiƙayi na masussuka da kaka. Iska kuwa ta kwashe su ta tafi da su, har ba a iya ganin ko alamarsu. Amma wannan dutse da ya buge mutum-mutumin ya girke, ya zama babban dutse ya cika duniya duka.

36. “Wannan shi ne mafarkin, yanzu kuma za mu faɗa wa sarki fassararsa.

37. Ya sarki, kai ne sarkin sarakuna wanda Allah na Sama ya ba ka sarauta, da iko, da ƙarfi, da daraja.

38. A hannunka kuma ya ba da dukan wurare inda 'yan adam, da dabbobi, da tsuntsaye suke zama. Ya sa ka ka mallake su duka. Kai ne kan zinariyan nan na mutum-mutumin.

39. A bayanka kuma za a yi wani mulki wanda bai kai kamar naka ba. Za a yi wani mulki kuma na uku mai darajar tagulla, wanda zai mallaki dukan duniya.

40. Za a kuma yi mulki na huɗu, mai ƙarfi kamar baƙin ƙarfe. Da yake baƙin ƙarfe yakan kakkarya, ya ragargaje abubuwa, haka nan wannan mulki zai ragargaje sauran mulkoki.

41. Ka kuma ga an yi ƙafafun da yatsotsin da baƙin ƙarfe gauraye da yumɓu, wato mulkin zai rabu, amma zai kasance da ƙarfi kamar na baƙin karfen da yake gauraye da yumɓu.

42. Kamar yadda yatsotsin ƙafafun rabi baƙin ƙarfe, rabi kuma yumɓu ne, haka nan mulkin zai kasance, rabi da ƙarfi, rabi kuma da gautsi.

Dan 2