Dan 2:27-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. Daniyel ya amsa wa sarki, ya ce, “Ba masu hikima, ko masu dabo, ko masu sihiri, ko masu duba, da za su iya su warware wa sarki wannan matsala da ta dame shi.

28. Amma akwai Allah a Sama mai bayyana asirai, shi ne ya sanar wa sarki Nebukadnezzar da abin da zai faru a kwanaki masu zuwa. Mafarkinka da wahayinka waɗanda suka zo cikin tunaninka, sa'ad da kake kwance bisa gadonka ke nan.

29. “Ya maigirma, sa'ad da kake kwance a gadonka sai tunanin abin da zai faru nan gaba ya zo maka. Shi kuma wanda yake bayyana asirai ya sanar da kai abin da zai faru nan gaba.

30. Amma ba a bayyana mini wannan asiri saboda ina da wata hikima fiye da sauran mutane ba, sai dai domin a sanar wa sarki da fassarar, ka kuma san tunanin da ya shiga zuciyarka.

31. “Ya sarki, ka ga wani babban mutum-mutum mai walƙiya, mai bantsoro, yana tsaye a gabanka.

32. An yi kan mutum-mutumin da zinariya tsantsa. Ƙirji da damutsa, an yi su da azurfa, cikinsa da cinyoyinsa, an yi su da tagulla.

33. Da baƙin ƙarfe aka yi sharaɓansa, an yi ƙafafunsa da baƙin ƙarfe gauraye da yumɓu.

Dan 2