2 Tas 2:14-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Domin wannan maƙasudi ya kira ku, ta wurin bishararmu, domin ku sami ɗaukakar Ubangijinmu Yesu Almasihu.

15. Saboda haka, 'yan'uwa, sai ku dage, ku kuma riƙi ka'idodin da muka koya muku kankan, ko da baka ko ta wurin wasiƙa.

16. To, Ubangijinmu Yesu Almasihu kansa, da kuma Allah Ubanmu, wanda ya ƙaunace mu, ya kuma ba mu madawwamiyar ta'aziyya da kyakkyawan bege ta wurin alherinsa,

17. yă ta'azantar da ku, ya kuma ƙarfafa ku ga yin kowane kyakkyawan aiki da magana.

2 Tas 2