14. Bayan haka sai ya gina garu a bayan garin Dawuda a yammacin Gihon, a kwari har zuwa Ƙofar Kifi, ya kewaye da shi zuwa Ofel, ya gina shi da tsayi sosai. Sa'an nan ya sa sarakunan yaƙi a garuruwa masu garu na Yahuza.
15. Ya kwashe gumaka da siffofi daga cikin Haikalin Ubangiji, da dukan bagadan da ya giggina a bisa dutse na Haikalin Ubangiji da a Urushalima. Ya zubar da su a bayan birnin.
16. Ya kuma komar da bagaden Ubangiji, ya miƙa hadayu na salama da na godiya, ya kuma umarci Yahuza ta bauta wa Ubangiji Allah na Isra'ila.
17. Duk da haka dai jama'a suka ci gaba da miƙa hadayunsu a masujadai, amma ga Ubangiji Allahnsu kaɗai.
18. Sauran ayyukan Manassa, da addu'o'insa zuwa ga Allahnsa, da abubuwan da masugani suka faɗa sa'ad da suka yi masa magana da sunan Ubangiji Allah na Isra'ila, suna cikin littafin tarihin sarakunan Isra'ila.
19. Addu'arsa, da yadda Allah ya karɓi roƙonsa, da dukan zunubinsa, da rashin amincinsa, da wuraren da ya gina masujadai, ya kafa Ashtarot da siffofi, kafin ya ƙasƙantar da kansa, suna nan a rubuce a littafin Hozai.
20. Haka fa Manassa ya rasu, suka binne shi a gidansa, sai Amon ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.
21. Amon yana da shekara ashirin da biyu sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi shekara biyu yana mulki a Urushalima.
22. Shi ma ya aikata mugunta a gaban Ubangiji yadda Manassa, tsohonsa, ya yi. Amon ya miƙa hadaya ga dukan siffofin da tsohonsa, Manassa, ya yi ya bauta musu.
23. Bai ƙasƙantar da kansa a gaban Ubangiji yadda tsohonsa, Manassa, ya yi ba, amma shi Amon ya yi ta yin zunubi a kai a kai.
24. Sai fadawansa suka yi masa maƙarƙashiya, suka kashe shi a gidansa.
25. Jama'ar ƙasar kuwa suka karkashe dukan waɗanda suka yi wa sarki Amon maƙarƙashiyar, suka naɗa Yosiya, ɗansa, ya gāji gadon sarautarsa.