2 Tar 31:2-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Hezekiya kuma ya raba firistoci da Lawiyawa kashi kashi, ko wanne da hidimarsa, firistoci da Lawiyawa, don hadayu na ƙonawa da na salama, su yi hidima a ƙofofin Ubangiji, don su yi godiya da yabo.

3. Daga dukiyarsa kuma ya ba da taimako na abin yin hadayun ƙonawa, wato hadayun ƙonawa na safe da na maraice, da hadayun ƙonawa na ranakun Asabar, da na amaryar wata, da na ƙayyadaddun idodi, kamar yadda aka rubuta a Attaura ta Ubangiji.

4. Hezekiya ya kuma umarci jama'ar da suke zaune a Urushalima su riƙa ba da rabon firistoci da na Lawiyawa, domin su mai da hankali ga dokar Ubangiji.

5. Nan da nan da aka baza labarin umarnin ko'ina, sai jama'ar Isra'ila suka ba da nunan fari na hatsinsu, da ruwan inabi, da mai, da zuma, da amfanin gona duka, suka kuma kawo zaka mai yawa ta kowane irin abu.

6. Jama'ar Isra'ila da na Yahuza waɗanda suke zaune a garuruwan Yahuza, su ma sun kawo tasu zaka ta shanu, da ta tumaki, da ta abubuwan da aka keɓe aka kuma tsarkake domin Ubangiji Allahnsu, suka tara su tsibi tsibi.

7. A wata na uku ne suka fara tattara tsibi tsibin, suka gama a wata na bakwai.

8. Sa'ad da Hezekiya da sarakuna suka zo suka ga tsibi tsibin, sai suka yabi Ubangiji da jama'arsa Isra'ila.

9. Hezekiya kuma ya yi wa firistoci da Lawiyawa tambaya a kan tsibi tsibin.

10. Sai Azariya, babban firist na gidan Zadok, ya amsa masa, ya ce, “Tun lokacin da suka fara kawo sadakarsu a Haikalin Ubangiji, mun ci mun ƙoshi, abin da ya ragu kuwa yana da yawa, gama Ubangiji ya sa wa jama'arsa albarka, saboda haka abin da ya ragu a rumbu yana da yawa.”

11. Sai Hezekiya ya umarce su su shirya ɗakuna a Haikalin Ubangiji, suka kuwa shirya.

12. Da aminci suka kawo sadakokinsu, ta zaka da ta keɓaɓɓun abubuwa. Babban shugaban da yake lura da su kuwa, shi ne Konaniya, Balawe, da Shimai ɗan'uwansa, shi ne na biyu,

2 Tar 31