3. Azariya yana da shekara goma sha shida sa'ad da ya ci sarauta. Ya kuwa yi mulki a Urushalima shekara hamsin da biyu, sunan tsohuwarsa Yekoliya ta Urushalima.
4. Azariya ya yi abin da yake daidai saboda Ubangiji, bisa ga dukan irin abin da tsohonsa Amaziya ya aikata.
5. Ya mai da hankalinsa ga bin Ubangiji a kwanakin Zakariya, wanda ya koya masa tsoron Allah. Dukan lokacin da yake bin Ubangiji, Allah ya wadata shi.
6. Azariya kuwa ya tafi ya yi yaƙi da Filistiyawa, ya rushe garun Gat, da na Yamniya, da na Ashdod. Ya giggina birane a ƙasar Ashdod, da waɗansu wurare na Filistiyawa.