2 Tar 24:15-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Yehoyada kuwa ya tsufa ƙwarai, ya yi tsawon rai, ya rasu. Ya rasu yana da shekara ɗari da talatin da haihuwa.

16. Suka binne shi a birnin Dawuda a inda ake binne sarakuna, saboda ya aikata nagarta a Isra'ila, da kuma a gaban Allah da Haikalin Allah.

17. Bayan rasuwar Yehoyada, sai sarakunan Yahuza suka zo suka yi mubaya'a a gaban sarki, sarki kuwa ya karɓa.

18. Sai suka ƙyale Haikalin Ubangiji Allah na kakanninsu, suka bauta wa Ashtarot da gumaka. Hasala kuwa ta auko a kan Yahuza da Urushalima, saboda wannan mugunta da suka yi.

19. Duk da haka Allah ya aika musu da annabawa don su komo da su wurinsa. Ko da yake sun shaida musu kuskurensu, duk da haka ba su kula ba.

20. Sai Ruhun Allah ya sauko wa Zakariya, ɗan Yehoyada, firist, ya tsaya a gaban jama'a ya yi magana da su, ya ce, “Ga abin da Allah ya ce, ‘Don me kuke ƙetare umarnan Ubangiji, har da za ku rasa albarka? Saboda kun rabu da bin Ubangiji, shi ma ya rabu da ku.’ ”

21. Amma suka yi masa maƙarƙashiya, sarki kuma ya ba da umarni, suka jejjefi annabin da duwatsu har ya mutu a farfajiyar Haikalin Ubangiji.

2 Tar 24