2 Tar 19:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Yehoshafat Sarkin Yahuza ya koma gidansa a Urushalima lafiya.

2. Sai Yehu maigani, ɗan Hanani, ya fita domin ya tarye shi, ya ce wa sarki Yehoshafat, “Za ka taimaki mugu ka kuma ƙaunaci maƙiyan Ubangiji? Saboda haka hasalar Ubangiji za ta same ka.

3. Duk da haka an sami wani abin kirki a wurinka, gama ka kawar da gumakan Ashtarot daga ƙasar, ka sa zuciyarka ga neman Allah.”

4. Yehoshafat ya yi zamansa a Urushalima, ya sāke shiga jama'a, tun daga Biyer-sheba har zuwa ƙasar tuddai ta Ifraimu, ya komar da su zuwa wurin Ubangiji, Allah na kakanninsu.

5. Sai ya naɗa alƙalai a ƙasar, a dukan biranen Yahuza masu kagara, birni birni.

6. Sai ya ce wa alƙalan, “Ku lura da abin da kuke yi, gama shari'ar da kuke yi ba ta mutum ba ce, amma ta Ubangiji ce, yana tare da ku sa'ad da kuke yanke shari'a.

2 Tar 19