2. Bayan 'yan shekaru sai ya kai wa Ahab ziyara a Samariya. Ahab kuwa ya yanka tumaki masu yawan gaske, da bijimai da yawa, domin Yehoshafat da mutanen da suke tare da shi. Ahab ya rinjaye shi don su fāɗa wa Ramot-gileyad da yaƙi.
3. Sai Ahab, Sarkin Isra'ila, ya ce wa Yehoshafat, Sarkin Yahuza, “Za ka tafi tare da ni zuwa Ramot-gileyad?”Sai ya amsa, ya ce, “Ni ma kamarka ne, jama'ata kuma kamar jama'arka ce, za mu je yaƙin tare da kai.”
4. Yehoshafat kuma ya ce wa Sarkin Isra'ila, “Sai ka nemi faɗar Ubangiji tukuna.”
5. Ahab kuwa ya tattara annabawa, mutum ɗari huɗu, ya ce musu, “Mu je mu faɗa wa Ramot-gileyad da yaƙi, ko in haƙura?”Sai suka ce, “Ka tafi, gama Allah zai ba da ita a hannun sarki.”
6. Amma Yehoshafat ya ce, “Ba wani annabin Ubangiji a nan wanda za mu tambaye shi kuma?”
7. Sai Sarkin Isra'ila ya ce wa Yehoshafat, “Akwai sauran mutum guda wanda za mu iya neman nufin Ubangiji daga gare shi, shi ne Mikaiya, ɗan Imla, amma na ƙi shi saboda ba ya yin annabcin kirki a kaina, sai dai na rashin alheri kullum.”Amma Yehoshafat ya ce, “Kada sarki ya faɗi haka.”
8. Sa'an nan Sarkin Isra'ila ya kira wani jarumi ya ce masa, “Maza ka kawo Mikaiya ɗan Imla.”
9. A sa'an nan Sarkin Isra'ila, da Yehoshafat, Sarkin Yahuza, suna zaune kowa a gadon sarautarsa, kowane ya caɓa ado, suna kuwa zaune a filin da yake ƙofar Samariya. Dukan annabawa kuwa suna ta yin annabci a gabansu.
10. Sai Zadakiya ɗan Kena'ana ya yi ƙahonin ƙarfe, ya ce, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Da waɗannan za ka sassoki Suriyawa har su hallaka!’ ”
11. Dukan annabawa kuma suka yi annabci, suna cewa, “Ka haura zuwa Ramot-gileyad ka ci nasara, gama Ubangiji zai ba da ita a hannun sarki.”
12. Jarumin fa da ya je ya kira Mikaiya ɗin, ya ce masa, “Ka kula fa, dukan maganganun da annabawa suke yi, sun yi wa sarki daɗi. Don haka kai ma ka yi maganar da za ta gamshi sarki kamar yadda suka yi.”
13. Amma Mikaiya ya ce, “Na rantse da Ubangiji abin da Allahna ya faɗa mini, shi zan faɗa.”
14. Da Mikaiya ya zo gaban sarki, sai sarki ya ce masa, “Mikaiya, mu haura zuwa Ramot-gileyad mu fāɗa mata da yaƙi, ko in haƙura?”Mikaiya kuwa ya amsa, ya ce, “Ka haura, gama za ka ci nasara, gama za a bashe su a hannunka.”
15. Amma sarki ya ce masa, “Har sau nawa zan rantsar da kai don kada ka faɗa mini kome, sai gaskiya da sunan Ubangiji?”
16. Mikaiya kuwa ya ce, “Ina ganin dukan Isra'ilawa a warwatse bisa tsaunuka, kamar tumakin da ba su da makiyayi. Ubangiji kuma ya ce, ‘Waɗannan ba su da makiyayi, bari dukansu, kowa ya koma gidansa da salama.’ ”
17. Sarkin Isra'ila fa ya ce wa Yehoshafat, “Ban faɗa maka ba, cewa ba zai yi annabcin alheri game da ni ba, sai na rashin alheri?”