16. Asa kuma ya tuɓe tsohuwarsa, Ma'aka, daga matsayinta na sarauniya don ta ƙera wata siffa mai banƙyama ta Ashtoret. Sai Asa ya sare siffar nan, ya niƙe ta, ya ƙone a rafin Kidron.
17. Amma ba a kawar da masujadan da yake Isra'ila ba, duk da haka zuciyar Asa sarai take, ba wani aibi duk kwanakinsa.
18. Sai ya shigar da sadakar da shi da tsohonsa suka keɓe don Haikalin Ubangiji, wato azurfa, da zinariya, da kwanoni da tasoshi, da finjalai iri iri.
19. Ba a kuma ƙara yin wani yaƙi ba har shekara ta talatin da biyar ta mulkinsa Asa.