30. Sai macen ta ce, “Na rantse da Ubangiji da kai kuma, ba zan bar ka ba.” Sai Elisha ya tashi, ya bi ta.
31. Gehazi kuma ya yi gaba, ya ɗora sandan a fuskar yaron, amma ba motsi ko alamar rai. Saboda haka ya koma, ya taryi Elisha, ya faɗa masa yaron bai farka ba.
32. Da Elisha ya kai ɗakin, ya ga yaron yana kwance matacce a gadonsa.
33. Sai ya shiga ya rufe ƙofa, daga shi sai yaron, ya yi addu'a ga Ubangiji.
34. Sa'an nan ya kwanta a kan yaron, ya sa bakinsa a bakin yaron, ya sa idanunsa a idanun yaron, hannuwansa kuma a kan na yaron, ya miƙe jikinsa akan yaron, sai jikin yaron ya yi ɗumi.
35. Elisha ya tashi, ya yi ta kai da komowa a cikin gidan, sa'an nan ya sāke hawan ɗakin, ya miƙe a kan yaron, sai yaron ya yi atishawa har sau bakwai, yaron kuma ya buɗe idanu.
36. Sai ya kira Gehazi ya ce, “Kirawo Bashunemiyar.” Sai ya kirawo ta. Da ta zo wurinsa, ya ce, “Ki ɗauki ɗanki.”
37. Ta kuwa zo, ta faɗi a gaban Elisha har ƙasa, sa'an nan ta ɗauki ɗanta, ta fita.
38. Elisha kuwa ya koma Gilgal sa'ad da ake fama da yunwa a ƙasar. Sa'ad da ƙungiyar annabawa suke zaune a gabansa, sai ya ce wa baransa, “Dora babbar tukunya, ka dafa wa annabawan nan fate-fate.”
39. Ɗaya daga cikinsu ya tafi saura don ya samo ganyayen ci. Sai ya ga yaɗon inabin jeji, ya ɗebo 'ya'yan ya rungumo cike da hannu, ya zo ya yanyanka ya zuba a tukunyar abinci, ba tare da sanin ko mene ne ba.
40. Amma da suka ɗanɗana, sai suka ta da murya suka ce, “Ya mutumin Allah, akwai dafi a cikin tukunyar nan!” Ba su iya cin abincin ba.
41. Sai Elisha ya ce, “To, ku kawo gari.” Aka kawo masa, ya kuwa zuba garin a tukunyar, sa'an nan ya ce, “Ku kwaso wa mutanen. Yanzu dai kome lafiya.”
42. Wani mutum ya zo daga Ba'alshalisha ya kawo wa annabi Elisha abinci na 'ya'yan fari, da dunƙule ashirin na sha'ir, da ɗanyun zangarkun hatsi. Sai Elisha ya ce wa baransa, ya ba ƙungiyar annabawa su ci,
43. amma baran ya ce, “Ƙaka zan raba wa mutum ɗari wannan abinci?”Elisha ya sāke cewa, “Ka ba mutane su ci, gama Ubangiji ya ce za su ci har su bar saura.”
44. Sai ya ajiye shi a gabansu. Suka ci, suka kuwa bar saura kamar yadda Ubangiji ya faɗa.