2 Sar 4:11-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Wata rana da Elisha ya zo, ya shiga ɗakin, ya huta.

12. Sai ya ce wa baransa, Gehazi, “Kirawo matan nan.” Da ya kirawo ta, sai ta zo ta tsaya a gabansa.

13. Ya ce wa Gehazi, “Ka tambaye ta me take so in yi mata saboda dukan wannan wahala da ta yi dominmu? Tana so in yi mata magana da sarki ko da shugaban sojoji?”Sai ta ce, “Ai, ina da dukan abin da nake bukata a cikin jama'ata.”

14. Elisha ya ce, “To, me za a yi mata?”Sai Gehazi ya amsa ya ce, “Ai, ba ta da ɗa, mijinta kuwa tsoho ne.”

15. Sai ya ce, “Kirawo ta.” Da ya kirawo ta, sai ta zo ta tsaya a ƙofar ɗakin.

16. Elisha kuwa ya ce mata, “Baɗi war haka za ki rungumi ɗa na kanki.”Sai ta ce, “A'a, ya shugabana, mutumin Allah, kada fa ka yi mini ƙarya.”

17. Amma macen ta sami juna biyu, ta kuwa haifi ɗa a daidai lokacin da Elisha ya faɗa mata.

18. Da yaron ya yi girma, sai wata rana ya bi mahaifinsa gona zuwa wurin masu girbi.

19. Sai ya ce wa mahaifinsa, “Wayyo, kaina, kaina.”Uban kuwa ya ce wa baransa, “Ka ɗauke shi, ka kai shi wurin uwar.”

20. Da aka ɗauke shi, aka kai wa uwar, sai ya zauna a cinyar uwar har rana tsaka, sa'an nan ya rasu.

21. Sai ta hau, ta kwantar da shi a gadon annabi Elisha, sa'an nan ta rufe ƙofa, ta fita.

22. Sa'an nan ta aika a faɗa wa mijinta, ta ce, “Ka aiko mini ɗaya daga cikin barori da jaki domin in tafi wurin annabi Elisha, zan komo da sauri.”

23. Sai ya ce, “Me ya sa za ki tafi wurinsa yau? Ai, yau ba amaryar wata ba ce, ba kuwa ranar Asabar ba ce.”Ita kuwa ta ce, “Ba kome, kada ka damu.”

24. Amma ta yi wa jakin shimfiɗa, ta kuma ce wa baranta, “Yi ta kora mini jakin, kada ka sassauta, sai na faɗa maka.”

25. Sai ta kama hanya, ta tafi wurin annabi Elisha a Dutsen Karmel.Sa'ad da annabi Elisha ya gan ta zuwa, sai ya ce wa Gehazi, wato baransa, “Duba, ga Bashunemiya can.

26. Ruga ka tarye ta, ka tambayi lafiyarta, da ta mijinta, da ta ɗanta.”Ta amsa, ta ce, “Lafiya ƙalau.”

27. Sa'ad da ta isa wurin annabi Elisha a kan dutsen, sai ta kama ƙafafunsa. Sai Gehazi ya zo zai ture ta. Amma mutumin Allah ya ce masa, “Ƙyale ta kurum, gama tana da baƙin ciki ƙwarai, Ubangiji kuwa ya ɓoye mini abin.”

2 Sar 4