2 Sar 25:2-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Aka kewaye birnin da yaƙi har shekara ta goma sha ɗaya ta sarautar Zadakiya.

3. A kan rana ta tara ga watan huɗu, yunwa ta tsananta a birnin gama ba abinci domin mutanen ƙasar.

4. Sai aka huda garun birnin, sarki da mayaƙa suka tsere da dare ta hanyar ƙofar da take tsakanin bango biyu kusa da gonar sarki, suka bi ta hanyar Araba, ko da yake Kaldiyawa suna kewaye da birnin.

5. Amma sojojin Kaldiyawa suka runtumi sarki suka kamo shi a filayen Yariko. Sojojinsa duka suka watse, suka bar shi.

6. Da suka kama sarkin, sai suka kawo shi wurin Sarkin Babila a Ribla, inda aka yanke masa hukunci.

7. Aka kashe 'ya'yansa maza a idonsa, sa'an nan aka ƙwaƙule masa idanu, aka kuma ɗaure shi da sarƙa, aka kai shi Babila.

8. A shekara ta goma sha tara ta sarautar Nebukadnezzar Sarkin Babila, a rana ta bakwai ga watan biyar, sai Nebuzaradan, mashawarcin sarki, shugaban sojojinsa kuma, ya shiga Urushalima.

9. Ya ƙone Haikalin Ubangiji, da gidan sarki, da dukan gidajen urushalima. Ya ƙone kowane babban gida.

10. Dukan sojojin Kaldiyawa waɗanda suke tare da shugaban, suka rushe garun da yake kewaye da Urushalima.

11. Sai Nebuzaradan shugaban sojojin, ya kwashe sauran mutanen da suka ragu a birnin, da waɗanda suka gudu zuwa wurin Sarkin Babila, da sauran da suka ragu, ya kwashe ya kai su zaman talala.

2 Sar 25