2 Sam 9:2-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Akwai wani bara na gidan Saul, sunansa Ziba. Sai aka kirawo shi wurin sarki Dawuda. Sarki ya tambaye shi, “Kai ne Ziba?”Sai ya amsa, “Ranka ya daɗe, ni ne.”

3. Sa'an nan sarki ya tambaye shi ko akwai wani wanda ya ragu daga gidan Saul, wanda zai nuna masa alherin Allah.Ziba ya ce wa sarki, “Akwai ɗan Jonatan, gurgu ne kuwa.”

4. Sai sarki ya tambaye shi, “Ina yake?”Ziba ya ce, “Yana gidan Makir, ɗan Ammiyel a Lodebar.”

5. Sarki kuwa ya aika aka zo da shi daga gidan Makir, ɗan Ammiyel, daga Lodebar.

6. Da aka zo da Mefiboshet, ɗan Jonatan, wato jikan Saul, sai ya rusuna har ƙasa, ya yi gaisuwa. Dawuda ya ce, “Mefiboshet!”Ya amsa, “Ranka ya daɗe, ga baranka.”

7. Dawuda ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, gama zan yi maka alheri ne saboda mahaifinka, Jonatan. Zan mayar maka da dukan gonakin kakanka, Saul. Kullum kuma za ka riƙa cin abinci a teburina.”

2 Sam 9