11. Dawuda ya keɓe wa Ubangiji kayayyakin nan tare da azurfa da zinariya da ya karɓe daga dukan al'umman da ya mallaka,
12. wato azurfa da zinariya na Edomawa, da na Mowabawa, da na Ammonawa, da na Filistiyawa, da na Amalekawa, da ganimar Hadadezer ɗan Rehob, Sarkin Zoba.
13. Dawuda kuwa ya yi suna. Ya kashe Edomawa dubu goma sha takwas (18,000) a kwarin Gishiri sa'ad da yake komowa.
14. Sai ya sa ƙungiyoyin sojoji a ƙasar Edom duka. Edomawa suka zama talakawan Dawuda. Ubangiji ya ba Dawuda nasara duk inda ya tafi.
15. Dawuda ya mallaki Isra'ila duka. Ya yi wa dukan jama'arsa shari'ar gaskiya da adalci.