2 Kor 2:2-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. To, in na sa ku baƙin ciki, wa zai faranta mini rai, in ba wanda na sa baƙin cikin ba?

3. Na rubuto muku haka ne, don kada in na zo, waɗanda ya kamata su faranta mini rai, ya zamana sun sa ni baƙin ciki. Domin na amince da ku duka, cewa farin cikina naku ne ku duka.

4. Na rubuto muku ne ina a cikin wahala da baƙin ciki gaya, har da hawaye mai yawa, ba don in sa ku baƙin ciki ba, sai dai domin ku san irin tsananin ƙaunar da nake yi muku.

5. Amma in wani ya jawo baƙin ciki, ba ni kaɗai ya jawo wa ba, amma ga wani fanni, sai in ce dukanku ne ya jawo wa, ba tsanantawa nake yi ba.

6. Irin mutumin nan, horon nan da galibin jama'a suka yi masa, ai, ya isa haka.

7. Gara dai ku yafe masa, ku kuma ƙarfafa masa zuciya, don kada gāyar baƙin ciki ya sha kansa.

8. Saboda haka, ina roƙonku ku tabbatar masa da ƙaunarku.

9. Na rubuto muku wannan takanas, domin in jarraba ku, in ga ko kuna yin biyayya ta kowace hanya.

10. Wanda kuka yafe wa kome, ni ma na yafe masa. Abin da na yafe kuwa, in dai har ma akwai abin yafewa, saboda ku ne na yafe masa, albarkacin Almasihu,

11. don kada Shaiɗan ya ribace mu, gama mu ba jahilan makidodinsa ba ne.

2 Kor 2