2 Kor 12:7-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Don kada kaina yă kumbura kuma saboda mafifitan wahayan da aka yi mini, sai aka saka mini wata cuta, wadda ta zama mini ƙaya, jakadan Shaiɗan, don yă riƙa wahalshe ni, don kada kaina ya kumbura.

8. Sau uku nake roƙon Ubangiji a kan wannan abu ya rabu da ni,

9. amma ya ce mini, “Alherina yā isa, domin ta wajen rashin ƙarfi ake ganin cikar ikona.” Saboda haka sai ma in ƙara yin alfarma da raunanata da farinciki fiye da na da, domin ikon Almasihu ya zauna a tare da ni.

10. Saboda haka, ina murna da raunanata, da cin mutuncin da ake yi mini, da shan wuya, da shan tsanani, da masifu saboda Almasihu, don sa'ad da nake rarrauna, a sa'an nan ne nake da ƙarfi.

11. Na yi wauta kam, amma ku ne kuke tilasta mini, ku ne kuwa ya kamata ku yaba mini, domin ba inda na kasa waɗannan mafifitan manzanni, ko da yake ni ba kome ba ne.

12. An gudanar da tabbatattun alamun manzo a cikinku ta matuƙar jimiri, da alamu da abubuwan al'ajabi da mu'ujizai.

13. Ta wace hanya ce kuka kasa sauran ikkilisiyoyi? Ko kuwa domin dai ni ban nauyaya muku ba? To, ku yafe mini wannan laifi!

2 Kor 12