1. An tilasta mini ne in yi gadara, ko da yake ba ta amfane ni da kome ba. Amma zan ci gaba da zancen ruya da wahayi da Ubangiji ya yi mini.
2. Na san wani mutum wanda yau shekara goma sha huɗu ke nan, aka ɗauke shi zuwa Sama ta uku bisa ga ikon Almasihu, ko yana a cikin jiki ne, ko ba a cikin jiki ba, ban sani ba, Allah ne masani.
3. Na kuma san mutumin nan, an ɗauke shi zuwa Firdausi, ko yana a cikin jiki ne, ko ba a cikin jiki ba, ban sani ba, Allah ne masani,
4. ya kuma ji waɗansu maganganu, waɗanda ba dama a faɗa, irin ma waɗanda ɗan adam ba shi da izinin faɗa.
5. Zan yi gadara da mutumin nan kam, amma ba zan yi gadara da kaina ba, sai dai ko da raunanata.
6. Ko da zan so yin gadara ma, ba zan zama wawa ba, gama gaskiya zan faɗa. Amma na bar zancen haka, don kada wani ya ɗauke ni fiye da yadda yake ganina, ko yadda yake jin maganata.
7. Don kada kaina yă kumbura kuma saboda mafifitan wahayan da aka yi mini, sai aka saka mini wata cuta, wadda ta zama mini ƙaya, jakadan Shaiɗan, don yă riƙa wahalshe ni, don kada kaina ya kumbura.