2 Kor 10:2-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. ina roƙonku kada ku tilasta ni in matsa muku sa'ad da na zo, gama na tabbata zan iya tsaya wa waɗanda suka ce abin da muke yi sha'anin duniya ne.

3. Ko da yake a cikin jiki muke tafiya, famarmu ba irin na mutuntaka ba ne.

4. Don kuwa makamanmu na fama ba na mutuntaka ba ne, na ikon Allah ne, masu rushe maƙamai masu ƙarfi.

5. Muna ka da masu hujjoji a cikin zace-zacensu, muna rushe kowace ganuwar alfarma mai tare sanin Allah, muna kuma jan hankalin kowa ga bautar Almasihu.

6. A shirye muke kuma mu hori kowane marar biyayya, muddin biyayyarku ta tabbata.

7. Ku dubi abin da yake bayyane mana! in dai wani ya amince na Almasihu ne, to, ya ƙara tunawa, wato kamar yadda yake shi na Almasihu ne, mu ma haka muke.

8. Ko da zan yi gadara fiye da kima a game da izinin nan namu, wanda Ubangiji ya bayar saboda inganta ku, ba don rushe ku ba, ba zan kunyata ba.

2 Kor 10