10. Mai ƙaunar ɗan'uwansa, a haske yake zaune, ba kuma wani sanadin sa tuntuɓe a gare shi.
11. Mai ƙin ɗan'uwansa kuwa, a duhu yake, a cikin duhu yake tafiya, bai san ma inda yake sa ƙafa ba, domin duhun ya makantar da shi.
12. Ya ku 'ya'yana ƙanana, ina rubuto muku ne domin an gafarta muku zunubanku saboda sunansa.
13. Ya ku dattawa, ina rubuto muku ne domin kun san shi, shi wanda yake tun fil'azal. Ya ku samari, ina rubuto muku ne domin kun ci nasara a kan Mugun nan. Ya ku 'yan yara, ina rubuto muku ne domin kun san Uba.
14. Ya ku dattawa, na rubuto muku ne domin kun san shi, shi wanda yake tun fil'azal. Ya ku samari, na rubuto muku ne domin kuna da ƙarfi, Maganar Allah tana zauna a zuciyarku, kun kuma ci nasara a kan Mugun nan.
15. Kada ku ƙaunaci duniya, ko abin da yake a cikinta. Kowa yake ƙaunar duniya, ba ya ƙaunar Uba ke nan sam.
16. Don kuwa duk abin da yake duniya, kamar su sha'awa irin ta halin mutuntaka, da sha'awar ido, da kuma alfarmar banza, ba na Uba ba ne, na duniya ne.