1 Tim 1:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Daga Bulus, manzon Almasihu Yesu bisa ga umarnin Allah Mai Cetonmu, da kuma na Almasihu Yesu abin begenmu,

2. zuwa ga Timoti, ɗana na hakika, ta wajen bangaskiya.Alheri, da jinƙai, da salama na Allah Uba, da na Almasihu Yesu Ubangijinmu su tabbata a gare ka.

3. Kamar yadda na roƙe ka, ka dakata a Afisa sa'ad da za ni ƙasar Makidoniya, ka gargaɗi waɗansu mutane kada su koyar da wata koyarwa dabam,

4. kada kuma su ɓata zarafinsu a wajen almara da yawan ƙididdigar asali marar iyaka, waɗanda sukan haddasa gardandami, a maimakon riƙon amanar al'amuran Allah da bangaskiya.

5. Alhali kuwa manufar gargaɗinmu ƙauna ce, wadda take bulbulowa daga tsarkakakkiyar zuciya, da lamiri mai kyau, da kuma sahihiyar bangaskiya.

6. Waɗansu sun kauce wa waɗannan al'amura, har sun bauɗe, sun shiga zancen banza.

1 Tim 1