1 Tar 4:21-43 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. 'Ya'yan Shela, maza, ɗan Yahuza, su ne Er wanda ya kafa garin Leka, da La'ada wanda ya kafa garin Maresha, da iyalan gidan masu aikin lilin da suke zaune a Bet-ashbeya,

22. da Yokim, da mutanen da suke zaune a Kozeba, da Yowash, da Saraf, waɗanda suka yi sarauta a Mowab, sa'an nan suka zauna a Baitalami. (Waɗannan labaru na tun dā ne.)

23. Su ne maginan tukwane, waɗanda suke zaune a Netayim da Gedera. Sun zauna tare da sarki don su yi masa aiki.

24. 'Ya'yan Saminu, maza, su ne Yemuwel, da Yamin, da Yakin, da Zohar, da Shawul,

25. da Shallum ɗansa, da Mibsam jīkansa, da Mishma jīkan ɗansa.

26. 'Ya'yan Mishma, maza, su ne Hammuwel, da Zakkur, da Shimai.

27. Shimai yana da 'ya'ya maza goma sha shida, da 'ya'ya mata shida, amma 'yan'uwansa ba su da 'ya'ya da yawa kamarsa. Iyalin Saminu ba su kai yawan na Yahuza ba.

28. Suka zauna a waɗannan garuruwa, wato Biyer-sheba, da Molada, da Hazar-shuwal,

29. da Bilha, da Ezem, da Eltola,

30. da Betuwel, da Horma, da Ziklag,

31. da Bet-markabot, da Hazarsusa, da Bet-biri, da Shayarim. Waɗannan su ne biranensu tun kafin Dawuda ya yi sarauta.

32-33. Sun kuwa zauna a waɗansu wurare guda biyar, wato Itam, da Ayin, da Rimmon, da Token, da Ashan, da ƙauyukan da suke kewaye, har zuwa kudu maso gabas da garin Ba'al: Ga lissafin iyalansu da wuraren da suka zauna.

34-37. Meshobab, da Yamlek, da Yosha ɗan Amaziya,Yowel, da Yehu ɗan Yoshibiya, wato jīkan Seraiya, ɗan Asiyel,Eliyehoyenai, da Ya'akoba, da Yeshohaya, da Asaya, da Adiyel, da Yesimiyel, da Benaiya,Ziza ɗan Shifi, wato jīkan Allon, zuriyar Yedaiya, da Shimri ɗan Shemaiya.

38. Waɗannan da aka jera sunayensu, su ne shugabannin iyalansu da gidajen kakanninsu.Sun ƙaru ƙwarai.

39. Suka yi tafiya har zuwa mashigin Gedor, zuwa gabashin kwarin don nemar wa garkunansu makiyaya.

40. A can suka sami makiyaya mai kyau mai dausayi. Ƙasar kuwa tana da faɗi, babu fitina, sai salama, gama mazaunan wurin a dā Hamawa ne.

41. Waɗannan da aka lasafta sunayensu, su ne suka zo a kwanakin Hezekiya Sarkin Yahuza, suka fāɗa wa alfarwai da bukkoki waɗanda suka tarar a can, suka hallaka su sarai, sa'an nan suka maye wurinsu saboda akwai makiyaya domin garkunansu a wurin.

42. Waɗansu daga cikinsu, mutum ɗari biyar daga zuriyar Saminu, suka tafi wajen gabashin Edom. Waɗanda suka shugabance su kuwa, su ne 'ya'yan Ishi, wato Felatiya, da Neyariya, da Refaya, da Uzziyel.

43. A can suka karkashe sauran Amalekawan da suka ragu, sa'an nan suka zauna a can har wa yau.

1 Tar 4