Ra'ubainu shi ne ɗan farin Isra'ila, amma saboda ya ƙazantar da gadon mahaifinsa aka ba 'ya'yan Yusufu, maza, ɗan Isra'ila, gādonsa na ɗan fari. Don haka ba a lasafta shi a kan matsayin ɗan fari ba.