4. Dukansu shida an haife su ne a Hebron inda ya yi sarauta shekara bakwai da wata shida.Ya yi sarauta a Urushalima shekara talatin da uku.
5. Waɗanda aka haifa masa a Urushalima, su ne Shimeya, da Shobab, da Natan, da Sulemanu, su huɗu ke nan waɗanda Bat-sheba 'yar Ammiyel ta haifa masa.
6. Yana da waɗansu 'ya'ya kuma, su ne Ibhar, da Elishuwa da Elifelet,
7. da Noga, da Nefeg, da Yafiya,
8. da Elishama, da Eliyada, da kuma Elifelet, su tara ke nan.
9. Waɗannan duka su ne 'ya'yan Dawuda, maza, banda 'ya'yan ƙwaraƙwarai. Tamar ita ce 'yar'uwarsu.
10. Waɗannan su ne zuriyar Sulemanu, daga Rehobowam, sai Abaija, da Asa, da Yehoshafat,
11. da Yoram, da Ahaziya, da Yowash,
12. da Amaziya, da Azariya, da Yotam,
13. da Ahaz, da Hezekiya da Manassa,
14. da Amon, da Yosiya.
15. 'Ya'yan Yosiya, maza, su ne Yohenan ɗan farinsa, na biyu shi ne Eliyakim, na uku shi ne Zadakiya, na huɗu shi ne Yehowahaz,