1 Tar 26:8-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Waɗannan duka iyalin Obed-edom ne. Su da 'ya'yansu maza da 'yan'uwansu suna da ƙarfi da gwaninta na yin aiki. Su sittin da biyu ne daga wajen Obed-edom.

9. Shallum yana da 'ya'ya maza da 'yan'uwa, su goma sha takwas jarumawa.

10. Hosa kuma na wajen 'ya'yan Merari, maza, yana da 'ya'ya maza, Shimri shi ne babba, ko da yake ba shi ne ɗan fari ba, duk da haka mahaifinsa ya maishe shi babba.

11. Hilkiya shi ne na biyu, da Tebaliya na uku, da Zakariya na huɗu. Dukan 'ya'yan Hosa, maza, da 'yan'uwansa, su goma sha uku ne.

12. Aka rarraba masu tsaron Haikali ƙungiya ƙungiya, bisa ga iyali, aka raba musu ayyuka a Haikali kamar dai sauran Lawiyawa.

13. Sai suka jefa kuri'a bisa ga gidajen kakanninsu, ba a damu da yawan jama'a a iyali ba, a kan kowace ƙofar.

14. Kuri'a ta ƙofar gabas ta faɗo a kan Shallum. Sai aka jefa kuri'a don ɗansa Zakariya, mai ba da shawara mai ma'ana, sai kuri'a ta ƙofar arewa ta faɗo a kansa.

15. Kuri'a ta ƙofar kudu ta faɗo a kan Obed-edom. Aka sa 'ya'yansa maza su lura da ɗakunan ajiya.

16. Kuri'a ta ƙofar yamma kusa da Ƙofar Shalleket, a kan hanyar da ta haura, ta faɗo a kan Shuffim da Hosa. Aka raba aikin tsaro bisa ga lokatan da aka tsara bi da bi.

17. A kowace rana Lawiyawa shida suke tsaron ƙofar gabas, huɗu a ƙofar kudu, huɗu kuma a ƙofar arewa, biyu biyu suke tsaron ɗakunan ajiya.

18. A ɗan ɗakin da take wajen yamma, akwai masu tsaro huɗu a hanyar, biyu kuma a ɗan ɗakin.

19. Waɗannan su ne ƙungiyoyin masu tsaron ƙofofi daga zuriyar Kora da ta Merari.

20. Sauran Lawiyawa, 'yan'uwansu kuwa, suke lura da baitulmalin Haikalin Allah, da ɗakin ajiyar kayan da aka keɓe ga Allah.

21. Libni daga cikin iyalin Gershon, shi ne kakan ƙungiyoyin iyali da dama, iyalin Yehiyel ne ɗaya daga cikinsu.

1 Tar 26