16. Kuri'a ta ƙofar yamma kusa da Ƙofar Shalleket, a kan hanyar da ta haura, ta faɗo a kan Shuffim da Hosa. Aka raba aikin tsaro bisa ga lokatan da aka tsara bi da bi.
17. A kowace rana Lawiyawa shida suke tsaron ƙofar gabas, huɗu a ƙofar kudu, huɗu kuma a ƙofar arewa, biyu biyu suke tsaron ɗakunan ajiya.
18. A ɗan ɗakin da take wajen yamma, akwai masu tsaro huɗu a hanyar, biyu kuma a ɗan ɗakin.
19. Waɗannan su ne ƙungiyoyin masu tsaron ƙofofi daga zuriyar Kora da ta Merari.
20. Sauran Lawiyawa, 'yan'uwansu kuwa, suke lura da baitulmalin Haikalin Allah, da ɗakin ajiyar kayan da aka keɓe ga Allah.
21. Libni daga cikin iyalin Gershon, shi ne kakan ƙungiyoyin iyali da dama, iyalin Yehiyel ne ɗaya daga cikinsu.
22. Biyu daga cikin wannan iyali, wato Zetam da Yowel, suke lura da baitulmalin Haikali da ɗakin ajiyar kaya.
23. Aka raba aiki kuma ga zuriyar Amram, da ta Izhara, da ta Hebron, da kuma ta Uzziyel.
24. Shebuwel ɗan Gershom, daga zuriyar Musa, shi ne babban jami'in baitulmalin.
25. Ta wurin ɗan'uwan Gershom, wato Eliyezer ya sami dangantaka da Shelomit. Eliyezer shi ne mahaifin Rehabiya, wanda ya haifi Yeshaya, uban Yoram, da Zikri, da Shelomit.
26. Shi wannan Shelomit da 'yan'uwansa suke lura da kyautai waɗanda sarki Dawuda, da shugabannin, gidajen kakanni, da shugabannin dubu dubu, da na ɗari ɗari, da shugabannin sojoji suka keɓe ga Allah.
27. Daga cikin ganimar yaƙi suka keɓe wani sashi domin gyaran Haikalin Ubangiji.
28. Dukan kuma abin da Sama'ila annabi, da Saul ɗan Kish, da Abner ɗan Ner, da Yowab ɗan Zeruya, suka keɓe an sa su a hannun Shelomit da 'yan'uwansa.
29. Kenaniya da 'ya'yansa maza na wajen Izhara su ne aka danƙa wa al'amuran sasantawa na Isra'ilawa, wato sun zama shugabanni da alƙalai.