1 Tar 22:11-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. “To, ɗana, Ubangiji ya kasance tare da kai, domin ka yi nasara ka gina Haikalin Ubangiji Allahnka, kamar yadda ya faɗa a kanka.

12. Ubangiji dai ya ba ka basira da haziƙanci domin sa'ad da ya sa ka ka lura da Isra'ila ka kiyaye dokokinsa.

13. Za ka arzuta idan ka kula ka kiyaye dokoki da ka'idodi da Ubangiji ya umarci Musa saboda Isra'ila. Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali. Kada ka ji tsoro, kada kuma ka karaya.

14. Da wahala mai yawa na yi tanadi domin Haikalin Ubangiji, zinariya wajen talanti dubu ɗari (100,000), da azurfa kuma wajen talanti zambar dubu (1,000,000), domin gina Haikalin Ubangiji. Bayan wannan akwai tagulla da ƙarfe masu tarin yawa. Na kuma tanada katakai da duwatsu. Kai kuma sai ka ƙara a kansu.

15. Kana da ma'aikata jingim, su masu fasa duwatsu, da magina, da masassaƙa, da gwanayen masu sana'o'i iri dabam dabam, masu yawan gaske.

16. Za su yi aiki da zinariya, da azurfa, da tagulla, da ƙarfe. Tashi, ka kama aiki, Ubangiji ya kasance tare da kai!”

17. Dawuda kuma ya umarci dukan shugabannin Isra'ila su taimaki ɗansa Sulemanu.

18. Ya ce, “Ubangiji Allahnku yana tare da ku, ya ba ku zaman lafiya a kowane sashi. Gama ya ba da mazaunan ƙasar a hannuna, an murƙushe ƙasar a gaban Ubangiji da jama'arsa.

19. Yanzu fa sai ku sa hankalinku da zuciyarku ga neman Ubangiji Allahnku. Ku tashi, ku gina wa Ubangiji Allah tsattsarkan wuri domin a kawo akwatin alkawari na Ubangiji, da tsarkakakkun tasoshin Allah a cikin Haikalin da aka gina saboda sunan Ubangiji.”

1 Tar 22