1 Tar 21:17-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Dawuda ya ce wa Allah, “Ai, ni ne na ba da umarni a ƙidaya jama'ar. Hakika, ni na yi zunubi, na kuwa aikata mummunan abu, amma waɗannan talakawa fa, me suka yi? Ya Ubangiji Allahna, ka bar hannunka ya yi gāba da ni da gidan tsohona, amma kada ka yi gāba da jama'arka, har da za ka aukar musu da annoba.”

18. Mala'ikan Ubangiji ya umarci Gad ya faɗa wa Dawuda ya haura, ya gina wa Ubangiji bagade a masussukar Arauna Bayebuse.

19. Dawuda kuwa ya haura kamar yadda Gad ya faɗa masa da sunan Ubangiji.

20. Arauna yana cikin sussukar alkama, sai ya waiwaya ya ga mala'ika. 'Ya'yansa maza su huɗu kuwa, waɗanda suke tare da shi suka ɓuya.

21. Sa'ad da Dawuda ya tafi wurin Arauna, da Arauna ya ga Dawuda, sai ya fito daga masussukar ya tafi ya fāɗi rub da ciki a gaban Dawuda ya gaishe shi.

22. Sai Dawuda ya ce masa, “Ka ba ni wannan masussuka don in gina wa Ubangiji bagade. Ka sayar mini da masussukar a bakin cikakken kuɗinta, domin a kawar wa jama'a da annobar.”

23. Arauna ya ce wa Dawuda, “Ka karɓa, na ba ka, sai ka yi abin da kake so da ita, ranka ya daɗe. Zan kuma ba da bijimai domin hadayu na ƙonawa, in ba da keken sussuka domin itacen wuta, in kuma ba da alkama don hadaya ta gari. Zan ba ka waɗannan duka.”

1 Tar 21