1. Dukan Isra'ilawa kuwa suka taru wurin Dawuda a Hebron, suka ce masa, “Mu ɗaya ne da kai.
2. Ko dā can lokacin da Saul yake sarauta, kai ne kake yi wa Isra'ilawa jagora zuwa yaƙi da komowa. Ubangiji Allahnka kuwa ya ce maka, ‘Za ka yi kiwon jama'ata, wato Isra'ilawa, ka kuma shugabance su.’ ”
3. Sai dattawan Isra'ilawa suka zo wurin sarki Dawuda a Hebron. Dawuda kuwa ya yi alkawari da su a Hebron a gaban Ubangiji, ake kuwa naɗa Dawuda ya zama Sarkin Isra'ila bisa ga faɗar Ubangiji ta bakin Sama'ila.
4. Sarki Dawuda kuwa, tare da dukan Isra'ilawa, suka tafi Urushalima, wato Yebus inda Yebusiyawa suke zaune.
5. Sai mazaunan Yebus, suka ce wa Dawuda, “Ba za ka shiga nan ba.” Duk da haka Dawuda ya ci Sihiyona, gari mai kagara, wato birnin Dawuda ke nan.
6. Sai Dawuda ya ce, “Duk wanda ya ci Yebusiyawa da fari shi ne zai zama babban shugaban sojoji.” Yowab ɗan Zeruya ne ya fara tafiya, domin wannan aka maishe shi shugaba.
7. Sa'an nan Dawuda ya zauna a kagara, don haka aka kira birnin, birnin Dawuda.
8. Sai ya rutsa birnin da gini tun daga Millo. Yowab kuma ya gyaggyara sauran birnin.
26-47. Waɗannan su ne manyan jarumawan sojoji.Asahel ɗan'uwan YowabElhanan ɗan Dodo daga BaitalamiShamma daga HarodHelez daga FeletAira ɗan Ikkesha daga TekowaAbiyezer daga AnatotSibbekai daga HushaIlai daga AhoMaharai daga NetofaHeled ɗan Ba'ana daga NetofaIttayi ɗan Ribai daga Gibeya ta BiliyaminuBenaiya na FiratonHurai daga rafuffuka kusa da Ga'ashAbiyel daga ArabaAzmawet daga BahurimEliyaba daga Shalim'Ya'yan Yashen, maza, daga GizonJonatan ɗan Shimeya daga HarodAhiyam ɗan Sharar daga HarodElifelet ɗan AhasbaiHefer daga MekaraAhaija daga FeletHezro daga KarmelNayarai ɗan EzbaiYowel ɗan'uwan NatanMibhar ɗan HagriZelek daga AmmonNaharai daga Biyerot (Mai riƙe wa Yowab ɗan Zeruya makamai)Aira da Gareb daga YattirUriya BahitteZabad ɗan AlaiAdina ɗan Shiza (Shi ne shugaba a kabilar Ra'ubainu, yana da ƙungiyarsa mai soja talatin tare da shi)Hanan ɗan Ma'akaYoshafat daga MitnaUzziya daga AshteraShama da Yehiyel 'ya'yan Hotam, maza, daga ArowerYediyel da Yoha 'ya'yan Shimri, maza, daga TizEliyel daga MahawaYeribai, da Yoshawiya 'ya'yan Elna'am, mazaItma daga MowabEliyel, da Obida, da Yawasiyel daga Zoba,