6. Sa'an nan Sarkin Isra'ila ya tara annabawa ɗari huɗu, ya tambaye su, ya ce, “In tafi in yi yaƙi da Ramot-gileyad, ko kuwa kada in tafi?”Su kuwa suka ce masa, “Ka haura, gama Ubangiji zai ba da ita a hannunka.”
7. Amma Yehoshafat ya ce, “Ba wani annabin da za mu tambaya kuma?”
8. Sarkin Isra'ila ya ce wa Yehoshafat, “Da sauran mutum ɗaya wanda za mu iya mu tambaya faɗar Ubangiji, shi ne Mikaiya ɗan Imla, amma ina ƙinsa, gama bai taɓa yin wani annabcin alheri a kaina ba, sai dai na masifa.”Yehoshafat ya ce, “Kada sarki ya faɗi haka.”
9. Sa'an nan Sarkin Isra'ila ya kirawo wani bafāde, ya ce masa, “Maza, ka taho da Mikaiya ɗan Imla.”
10. Sarkin Isra'ila da Yehoshafat, Sarkin Yahuza, suna zaune a kujerun sarautarsu, saye da tufafinsu a dandalin ƙofar Samariya. Annabawa kuwa suna annabci a gabansu.
11. Zadakiya ɗan Kena'ana ya yi ƙahonin ƙarfe, ya ce, “Ubangiji ya ce, ‘Da waɗannan ƙahoni za ka tunkuyi Suriyawa har su hallaka.’ ”
12. Dukan annabawan suka yi annabci iri ɗaya, suna cewa, “Ka haura zuwa Ramot, za ka yi nasara, gama Ubangiji zai ba da ita a hannunka.”
13. Bafāden da ya tafi kiran Mikaiya ya ce masa, “Ga shi, maganar sauran annabawan iri ɗaya ce, sun yi maganar alheri ga sarki, sai kai ma ka yi magana irin tasu, ka yi maganar alheri ga sarki.”
14. Amma Mikaiya ya ce, “Na rantse da Ubangiji, abin da Ubangiji ya faɗa mini, shi ne zan faɗa.”
15. Da ya zo gaban sarki, sai sarki ya ce masa, “Mikaiya, mu tafi Ramot don yaƙi, ko kuwa kada mu tafi?”Ya amsa masa ya ce, “Ka haura, za ka yi nasara, Ubangiji zai ba da ita a hannunka.”
16. Sarki Ahab kuwa ya ce masa, “Sau nawa zan roƙe ka kada ka faɗa mini kome sai dai gaskiya ta Ubangiji?”
17. Mikaiya ya ce, “Na ga mutanen Isra'ila duka a warwatse a kan tuddai kamar tumakin da ba su da makiyayi, Ubangiji kuwa ya ce, ‘Waɗannan ba su da shugaba, bari kowa ya koma gidansa lafiya.’ ”
18. Sarkin Isra'ila ya ce wa Yehoshafat, “Ban faɗa maka ba, ba zai yi wani annabcin alheri a kaina ba sai dai na masifa?”