39. Sauran ayyukan Ahab da dukan abin da ya yi, da gidan da ya gina na hauren giwa da garuruwan da ya gina, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.
40. Ahab ya rasu kamar kakanninsa. Ɗansa Ahaziya ya gāji sarautarsa.
41. Yehoshafat ɗan Asa ya ci sarautar Yahuza a shekara ta huɗu ta sarautar Ahab, Sarkin Isra'ila.
42. Yehoshafat yana da shekara talatin da biyar sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi shekara ashirin da biyar yana sarauta a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Azuba 'yar Shilhi.
43. Ya bi halin tsohonsa, Asa, bai karkace ba. Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji. Duk da haka ba a rushe wuraren tsafin na tuddai ba. Mutane suka yi ta miƙa hadayu, suka ƙona turare a tuddan.
44. Yehoshafat kuma ya ba Sarkin Isra'ila amana.
45. Sauran ayyukan Yehoshafat, da ƙarfin da ya nuna, da yadda ya yi yaƙi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.
46. Ya kori dukan karuwai mata da maza da suka ragu a ƙasar a zamanin tsohonsa Asa.
47. A lokacin babu sarki a Edom sai wakili.
48. Yehoshafat ya yi jiragen ruwa a Tarshish don su tafi Ofir su kwaso zinariya, amma jiragen ba su tafi ba, gama jiragen sun farfashe a Eziyon-geber.
49. Sa'an nan Ahaziya, ɗan Ahab, ya ce wa Yehoshafat. “Ka bar barorina su tafi tare da naka a cikin jirage.” Amma Yehoshafat bai yarda ba.
50. Yehoshafat kuwa ya rasu, aka binne shi a inda aka binne kakanninsa a birnin kakansa Dawuda. Ɗansa Yehoram ya gaji sarautarsa.