1 Sar 20:18-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Sai ya ce, “Ku kama su da rai, ko sun zo da nufin salama ko da na yaƙi.”

19. Waɗannan kuwa suka fita daga birnin, wato sojoji matasa, rundunar Isra'ilawa kuma tana biye da su,

20. kowa ya kashe abokin gābansa. Suriyawa kuwa suka gudu, Isra'ilawa kuma suka runtume su. Amma Ben-hadad, Sarkin Suriya, ya tsere kan doki tare da mahayan dawakai.

21. Sarkin Isra'ila ya fita, ya ƙwace dawakai da karusai, ya kashe Suriyawa da yawa.

22. Sa'an nan annabin ya je wurin Sarkin Isra'ila, ya ce masa, “Tafi, ka ƙarfafa kanka, ka yi tunani sosai a kan abin da za ka yi, gama da juyawar shekara Sarkin Suriya zai kawo maka yaƙi.”

23. Fādawan Sarkin Suriya suka ce masa, “Allolinsu na tuddai ne, don haka suka fi mu ƙarfi, bari mu yi yaƙi da su a cikin kwari, ta haka za mu ci su ba shakka.

24. Yanzu abin da za ka yi ke nan, sai ka fitar da sarakuna daga matsayinsu, ka sa shugabannin sojoji maimakonsu.

25. Sa'an nan ka tara sojoji kamar yawan waɗanda ka rasa, ka kuma tara dawakai a maimakon na dā, da karusai a maimakon karusai na dā. Mu kuwa za mu yi yaƙi da su a kwari. Ba shakka za mu ci su.”Sarki Ben-hadad ya ji maganarsu, ya kuwa yi haka nan.

26. Da shekara ta juyo, sai Ben-hadad ya tara Suriyawa, suka haura zuwa Afek don su yi yaƙi da Isra'ilawa.

27. Aka tara mutanen Isra'ila, aka ba su guzuri, suka tafi, su yi yaƙi da Suriyawa. Isra'ilawa suka kafa sansani a gabansu kamar 'yan garkuna biyu na awaki, amma Suriyawa suka cika ƙasar.

28. Annabin Allah kuwa ya je wurin Sarkin Isra'ila ya ce masa, “Ubangiji ya ce, ‘Tun da yake Suriyawa sun ce, Ubangiji shi Allah na tuddai ne, ba Allah na kwari ba, saboda haka zan ba da dukan wannan taron jama'a a hannunka, za ka sani ni ne Ubangiji.’ ”

1 Sar 20