14. Ubangiji kuma zai ta da wani wanda zai sarauci Isra'ila, wanda kuma zai rushe gidan Yerobowam daga yanzu har zuwa nan gaba.
15. Ubangiji zai hukunta Isra'ila kamar yadda akan girgiza iwa a baƙin rafi, zai tumɓuke Isra'ila daga wannan ƙasa mai albarka wadda ya ba kakanninsu, ya kuma watsar da su a hayin Kogin Yufiretis, domin sun yi wa kansu gumaka don sun tsokani Ubangiji ya yi fushi.
16. Ubangiji zai rabu da Isra'ila saboda zunuban Yerobowam waɗanda ya yi, da kuma waɗanda ya sa mutanen Isra'ila su yi.”
17. Sa'an nan matar Yerobowam ta tashi, ta tafi Tirza. Amma tana shiga gidan ke nan, sai yaron ya mutu.
18. Jama'ar Isra'ila duka suka binne shi, suka yi makoki dominsa, kamar yadda Ubangiji ya faɗa ta bakin bawansa, annabi Ahija.
19. Sauran ayyukan Yerobowam, da yaƙe-yaƙensa, da yadda ya yi mulki, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.
20. Yerobowam ya yi mulki shekara ashirin da biyu sa'an nan ya rasu, aka binne shi. Ɗansa Nadab ya gāji sarautarsa.
21. Rehobowam ɗan Sulemanu ya yi mulki a Yahuza. Yana da shekara arba'in da ɗaya sa'ad da ya ci sarauta. Ya kuwa yi shekara goma sha bakwai yana sarauta a Urushalima, birnin da Ubangiji ya zaɓa daga cikin kabilan Isra'ila duka, domin ya sa sunansa ya kasance a wurin. Sunan tsohuwarsa Na'ama, ita kuwa Ba'ammoniya ce.
22. Mutanen Yahuza suka yi wa Ubangiji zunubi. Suka tsokane shi ya yi fushi saboda zunuban da suka aikata fiye da abin da kakanninsu suka yi.
23. Gama su ma sun gina wa kansu wuraren tsafi a tuddai, da ginshiƙai, da gumaka a tuddai, da cikin duhuwar itatuwa.
24. Fiye da haka kuma akwai mata da maza da suke aikin karuwanci a wuraren da suke tsafin a wurin al'ummai. Mutanen Yahuza sun yi dukan abubuwan ƙazanta na al'ummai waɗanda Ubangiji ya kora sa'ad da Isra'ilawa suke gab da shigar ƙasar.