1 Sar 1:38-49 Littafi Mai Tsarki (HAU)

38. Saboda haka sai Zadok, firist, da annabi Natan, da Benaiya ɗan Yehoyada, da masu tsaron lafiyar sarki, suka tafi, suka sa Sulemanu ya hau alfadarin sarki Dawuda. Suka kuma kai shi Gihon.

39. A can ne Zadok, firist, ya ɗauki ƙahon mai wanda ya kawo daga alfarwa ta sujada, ya zuba wa Sulemanu. Sa'an nan suka busa ƙaho, dukan mutane kuwa suka ce, “Ran sarki Sulemanu ya daɗe.”

40. Mutane duka kuwa suka bi shi, suna bushe-bushe, suna murna da yawa, kamar ƙasa ta tsage saboda sowarsu.

41. Adonija da dukan baƙin da suke tare da shi suka ji amon sowa bayan da suka gama cin abinci. Da Yowab ya ji busar ƙaho, sai ya ce, “Mene ne dalilin wannan hargitsi a birni?”

42. Yana cikin magana ke nan sai ga Jonatan ɗan Abiyata, firist, ya zo. Adonija ya ce musu, “Shigo, gama kai nagarin mutum ne, ka kawo albishir.”

43. Jonatan kuwa ya ce wa Adonija, “A'a, gama ubangijinmu, sarki Dawuda, ya naɗa Sulemanu sarki.

44. Sarki ya aiki Zadok, firist, da annabi Natan, da Benaiya ɗan Yehoyada, da masu tsaron lafiyar sarki. Su kuwa suka sa Sulemanu ya hau alfadarin sarki.

45. Zadok firist, da annabi Natan kuma suka zuba masa mai a Gihon don ya zama sarki. Daga can suka tashi da murna don haka ake hayaniya a birnin. Wannan ita ce hayaniyar da kake ji.

46. Sulemanu ne sarki yanzu.

47. Banda wannan kuma, fādawa sun tafi su kai caffa ga sarki Dawuda, suna cewa, ‘Allahnka ya sa Sulemanu ya yi suna fiye da kai, ya kuma fīfita gadon sarautarsa fiye da naka.’ Sai sarki ya sunkuyar da kansa a gadonsa.

48. Sa'an nan ya ce, ‘Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah na Isra'ila wanda ya sa ɗaya daga cikin zuriyata ya hau gadon sarautata yau, idona kuwa ya gani.’ ”

49. Sai baƙin Adonija duka suka tashi suna rawar jiki, kowa ya kama hanyarsa.

1 Sar 1