1 Sam 19:23-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Sai ya tashi daga can zuwa Nayot ta Rama. Ruhun Allah kuwa ya sauko a kansa, sai shi kuma ya shiga yin annabci har ya kai Nayot ta Rama,

24. ya kuma tuɓe tufafinsa, ya yi ta annabci a gaban Sama'ila. Ya kwanta huntu dukan yini da dukan dare. Don haka aka riƙa yin karin magana da cewa, “Har Saul ma yana cikin annabawa?”

1 Sam 19