29. Dawuda kuwa ya ce, “To, me kuma na yi, ba tambaya kawai na yi ba?”
30. Sai ya rabu da shi ya tafi wurin wani, ya sāke yin tambaya irin ta dā, mutane kuma suka ba shi amsa irin ta dā.
31. Sa'ad da waɗansu suka ji maganar da Dawuda ya yi, sai suka faɗa wa Saul. Shi kuwa ya aika a kira Dawuda.
32. Dawuda kuwa ya ce wa Saul, “Kada zuciyar kowa ta karai saboda wannan mutum, baranka zai tafi ya yi yaƙi da shi.”
33. Saul ya ce wa Dawuda, “Ba za ka iya yaƙi da wannan Bafiliste ba, gama kai ɗan saurayi ne, shi kuwa ya saba da yaƙi tun yana saurayi.”