9. Wata rana a Shilo bayan da sun gama cin abinci, sai Hannatu ta tashi. Eli, firist, kuwa yana zaune a kujera a bakin ƙofar masujadar Ubangiji.
10. Hannatu tana fama da baƙin ciki ƙwarai, sai ta yi addu'a, tana kuka da ƙarfi ga Ubangiji.
11. Ta yi wa'adi, ta ce, “Ya Ubangiji Mai Runduna, idan lalle ka dube ni, ni baiwarka, ka tuna da ni, ba ka manta da ni baiwarka ba, amma ka ba ni ɗa, ni ma sai in ba da shi ga Ubangiji dukan kwanakinsa, aska kuwa ba za ta taɓa kansa ba.”
12. Eli kuwa ya lura da bakin Hannatu sa'ad da take yin addu'a.
13. Gama ta yi addu'ar a zuci, ba a jin muryarta, sai dai leɓun motsi. Don haka Eli ya zaci tana maye ne,
14. ya kuwa ce mata, “Sai yaushe za ki daina maye? Ki daina shan ruwan inabi.”
15. Hannatu kuwa ta amsa ta ce, “Ba haka ba, ya shugabana, ni mace ce da take baƙin ciki ƙwarai. Ni ban sha ruwan inabi, ko wani abu mai sa maye ba, amma ina faɗa wa Ubangiji dukan abin da yake a zuciyata.
16. Kada ka zaci ni 'yar iska ce. Ni dai ina faɗar damuwata da tsokanar da ake yi mini ne.”
17. Sai Eli ya ce mata, “Ki sauka lafiya, Allah na Isra'ila ya amsa miki roƙonki.”
18. Ita kuma ta amsa, ta ce, “Bari baiwarka ta sami tagomashi a gare ka.” Sa'an nan ta tafi, ta ci abinci. Ba ta ƙara ɓata ranta ba.
19. Elkana da iyalinsa suka tashi tun da sassafe suka yi wa Ubangiji sujada, sa'an nan suka koma gidansu a Rama. Elkana fa ya kwana da matarsa, Hannatu. Ubangiji kuwa ya tuna da ita.
20. Ta yi juna biyu, ta haifa ɗa, ta raɗa masa suna Sama'ila, wato “Na roƙo shi daga wurin Ubangiji.”
21. Elkana da iyalinsa duka suka tafi Shilo domin su miƙa wa Ubangiji hadaya ta shekara shekara, ya kuma cika wa'adinsa.
22. Amma Hannatu ba ta tafi ba, sai ta ce wa mijinta, “Da zarar an yaye yaron, zan kai shi domin ya zauna a gidan Ubangiji muddin ransa.”
23. Elkana ya ce mata, “Ki yi abin da kika ga ya fi kyau, ki jira har ki yaye shi, Ubangiji dai ya cika maganarsa.” Hannatu ta tsaya a gida, ta yi ta renon ɗanta.
24. Sa'ad da ta yaye yaron, sai ta ɗauke shi, ta kuma ɗauki bijimi bana uku, da mudun gari, da salkar ruwan inabi, ta kai shi ɗakin Ubangiji a Shilo, yaron kuwa yana ɗan ƙarami.
25. Sai suka yanka bijimin, suka kuma kai yaron wurin Eli.